Compiled by Umar Dalha.
🏰🏰🏰🏰
            DAN SARKI
            🏰🏰🏰🏰
Written by Firdausi M Auwal
Edited by Aisha Muhammad (Mzz Daddy)
بسم الله الرحمن الرخيم
*Na fara wannan littafin da sunan Allah mai rahama mai jin kai*
*Wannan littafin ba nayishi bane dan cin zarafin wani ko wata ba, saboda haka duk wanda yaga wani abu yayi kamada yanayin rayuwarshi a ciki toh akasi aka samu*
                  0⃣1⃣
             Motocine sunkai guda goma shabiyu suna tafiya cikin kwanciyar hankali akan hanya kamar basuson motsawa  wanda ke sauri baxai iya bin irin wanna tafiyar ba. 
Bakin wani  katon gate naga sun tsaya,  sai naga wani rubutu jikin gate din,  sai da nakalla sosai naga an rubuta " *MASARAUTAR ZAZZAU*". 
            Ina cikin kallon naga anbude gate din, motocin  suka shiga daya bayan daya a tsanake banyan sunyi parking naga gaba daya kuyangi da barorin dake gurin sun zo sunyi tsaye cikin layi fadawan dake cikin motocin da bodyguards din suma suka fito suka tsaye amma nacikin mota banga kowaye ba.(a zuciya nace amma wannan yarinyar akwai jan aji)
           30 mints latter 
            Suna nan tsaye basu bar gurin ba kuma nacikin mota bai fito ba sai kawai gani nayi anbude motar akasalan ce, MASHA-ALLAH  shine kawai abunda naji bakina ke iya furtawa a lokacin da idanuna suka yi tazalo da wani kyakkyawan hannu banyan kamar sec. 30 sai,  ainihin mai hannun yafito(ashe) namijine kai wannan kasaita haka, fitowar shi yayi dai dai da lokacin da kuyangi., barori harmada fadawan ke gaidashi amma saboda kasaita kamar ma ba da shi suke ba nan ne fa aka fara kirari DAN SARKI jikan SARKI  yarima me jiran gado badon angaji da SARKI ba sai don haka abun yake sai, alokacin yadaga musu hannu alamun su dai na saboda shi ya tsani yawan magana ko bashi keyiba. 
          Kofar wani guri naga anbude mashi yashiga wani palour ne yashiga mai masifar kyau komai na palourn white ne tiles din gurin yana walkiya saboda samun gyara ga fararen bubs na haska gurin,  kaitsaye ya wuce sai naga ya nufi wata kofa ya bide wannan karon da kanshi ya bude saboda sashen ma kamar ba kowa aciki wani corridor naga yabi sai yashiga wani palourn kuma wannan kam milk ne paint din sai kujeru red da touches din white acikine naga wata Mata mai Dan shekaru amma gayu da hutu sun boye shekarun kishingide take akan tumtum  shima kalar gujerun gurin nega kayan marmari agaban ta tanaci cikin kwanciyar hankali, ya xo ya duka gabanta sai yan xu na ji muryar shi irin lion 🦁 voice dinnan mai dadin sauraro na jaruman maxa yana cewa the only barka da gida ta dago ta kalleshi da murmushi akan fuskarta tace lafiya qalau, ykk, ya aiki.? Ya dan yamutse fuska yace alhmd. Daganan ya Samu guri ya xauna bai koma magana ba,  maman tashi tasani sarai yunwace ta  xaunarda shi amma baxai iya cewa akawo mishi abinci ba, sai ta daga murya naji tana cewa Balkisu!  Balkisu!!  Can na tsinkayi wata karamar murya na cewa na'am, Subhan -Allah wata kyakyawar yarinya yace da ba xata wuce 19 years ba ta fito a hanxarce taxo ta duka bata ma lura da wanda ke zaune gurin ba shi koh dan mulkin sai zabga mata harara yake yi don bata gaida shi ba umman ce ta kula tace baki gaida " *ARYAN*" ba, ta dago da sauri tace sannu da hutawa yarima yayi shiru ya kyaleta ita dinma bata da mu da ya amsa ba Umma tace jeki kawoma yarima abinci harta tashi sai taji yana cewa gaskiya the only baxan iya ciba inba ke kika kawo ba ta kalleshi ta ce Aryan.......... 


